2015: An musanta bai wa malamai kudi

Konannen gini a Kaduna sakamakon rikicin siyasa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Konannen gini a Kaduna sakamakon rikicin siyasa

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan addinin musulinci ya musanta zargin da ake yi cewa mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo ya yi taruka da malamai ne domin kira su zabe Goodluck Jonathan, yana mai cewa an yi tarukan ne domin samun zaman lafiya.

An dai gudanar da tarukan ne a jahar Kaduna da sunan kokarin samar da zaman lafiya, sai dai lamarin ya ja hankulan 'yan kasar wadanda suka yi zargin cewa an yi ne domin neman goyon bayan malamai su zabi shugaba Jonathan na haifar da cece kuce.

Yawancin malamain da BBC ta tuntuba sun ki yin magana a kan tarukan, sai dai wani babban malami da bai amince a fadi sunasa ba ya ce bai ga illar yin irin wannan taro ba.

A zaben shekarar 2011 ma an zargin malamai da sarakuna da karbar kudi domin zaben shugaba Jonathan.

Karin bayani