Ana gab da samun maganin cutar HIV

Masu fama da cutar HIV a Malawi Hakkin mallakar hoto z
Image caption Masu fama da cutar HIV a Malawi

Wata sabuwar hanya da aka bullo da ita ta riga-kafi, ga alama ta kare Birai daga kamuwa da kwayar cutar HIV kamar yadda rahoton masana kimiyya na Amurka ya nuna.

Yawanci dai, magungunan riga-kafi suna ba da horo ne ga tsarin garkuwar jiki wajen yaki da shigar kwayoyin cututtuka.

A maimakon haka, masu bincike a cibiyar bincike ta Scripps dake California sun dan jirkita kwayar halitta ta Birai, don sanya ma jikinsu sinadaran yaki da cutar HIV.

Tawagar masu bincken ta bayyana wannan aiki a matsayin wani namijin yunkuri kuma suna son nan ba da jimawa ba za a fara gwaji ga 'yan adam.

Kwararru masu zaman kansu a wannan fanni sun ce, wannan shawara babbar abin dubawa ce.

Hanyar da aka bi ta yi amfani da tiyatar wani bangare ne na jiki, inda ta sanya wata kwayar halitta da nufin yin wannan gwaji.

Wannan bangare da aka sanya kwayar halittan ta kunshi hanyoyin da za a bi na kawar da kwayar cutar HIV, wadda aka rinka durawa a hanyar jini.

Gwajin wanda aka bayar da rahotonsa a mujallar halittu ta nuna yadda aka baiwa Biran kariya daga kamuwa da kwayar cutar HIV har tsawon a kalla makonni 34.

Kasancewar kuma akwai kariya ta shigar da kwayar cutar fiye da kiima, kwatankwacin adadin sabuwar kwayar cutar da za ta iya yaduwa a jikin majiyyaci kwayar cutar ta HIV, masu binciken sun yi imanin cewa za a iya amfani da wannan hanya wajen mutanen dake dauke da kwayar cutar ta HIV.

Jagoran masu binciken Farfesa Michael Farzan ya gaya ma BBC cewa "muna gab da samun nasara fiye da kwacce hanyar da aka bi a duniya ta bayar da kariya daga cutar HIV, to amma har yanzu da sauran aiki, kamar na sanin yadda za a bayar da kariya wajen bayar da wadannan magunguna ga mutane masu yawa.

Karin bayani