Niger za ta yi bincike kan kisan mutane

Image caption Gwamnatin Nijar ta yi jaje ga iyalan mutanen da suka mutu.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce za ta gudanar da cikakken bincike a kan kisan da wani jirgin yaki ya yi wa mutane 37 da ke zaman makoki a wani kauye da ke yankin Abadam na kasar.

A ranar Laraba ne dai jirgin ya yi luguden wuta kan mutanen, lamarin da wasu ke ganin ya yi zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Baya ga mutanen da suka mutu, mataimakin magajin garin Abadam, Ibrahim Ari, ya shaida wa BBC cewa fiye da mutane 20 ne suka jikkata sakamakon harin.

Malam Ibrahim ya kara da cewa jirgin yaki ya saki bama-bamai uku ne, daya ya fada a tsakiyar masu zaman makokin, yayin da biyu kuma suka fashe a wajen gari.

Za a yi zaman makoki

Sai dai a wani taron manema labarai da ya yi ranar Laraba da daddare, kakakin gwamnatin kasar, Malam Marou Amadou, ya ce za su tabbatar an yi adalci a binciken da za su yi.

A cewarsa, binciken nasu zai hada da gano ainihin jirgin wacce kasa ce ya kai harin.

Ya kuma yi jaje ga iyalan mutanen da lamarin ya rutsa da su, yana mai cewa gwamnati za ta ba su tallafin da ya dace.

Gwamnatin ta kuma ware kwanaki uku domin a yi zaben makoki a kasar.