Darajar Naira ta ci gaba da faduwa

Image caption Naira na tsaka mai wuya a wannan lokacin

Babban Bankin Nigeria- CBN ya daina tsarinsa na sayar da dalar Amurka ga masu bukatarta da ya kan yi sau biyu a kowane mako a kan farashi mai sauki.

A halin yanzu za a sayar da ita ne a wani tsari na kasuwancin tsakanin banki da banki matakin wasu masu sharhi ke cewar tamkar rage darajar Naira ne.

Tun farko dai babban bankin kasar ya rage darajar Nairar, sakamakon faduwar farashin mai da kuma raguwar kudin wajen da kasar ke samu.

Tun daga farkon wannan shekarar, darajar Naira ke ta faduwa idan aka kwatanta da kudaden kasashen waje kamar dalar Amurka da fan na Ingila.