Ba da musulunci muke yaki ba — Obama

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr Obama ya bukaci kasashen duniya su tashi tsaye dan yakar ayyukan ta'addanci.

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce duniya na yin yaki da 'yan ta'adda ne wadanda suka fandarewa Musulunci, ba da addinin musuluncin ba.

Mr Obama ya bayyana haka ne a wani taro kan yaki da ta'addanci na kwanaki uku a birnin Washington,.

Ana yin taron ne domin nemo hanyoyin da za a dakile ayyukan masu tayar da kayar baya a duniya.

Shugaba Obama ya ce dole ne duniya ta tashi tsaye ta tunkari munanan akidoji wadanda kungiyoyi irin su IS ke amfani da su wajen tsokano tashin hankali da kuma cusawa matasa mummunar akida.

Ya kara da cewa lallai ne a dauki matakan kawar da matsalolin da ke sanya wa matasa suna shiga cikin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.

Wakilai daga kasashe fiye da sittin ne suka halarci wannan taro, hakan kuma ya biyo bayan hare-haren da aka kai kasashen Denmark da Faransa da kuma Australia.