Rikici ya rincaɓe a gabashin Ukraine

Hakkin mallakar hoto
Image caption An samu cikas a yunkurin tsagaita wuta

An tsananta kai hare-hare da makaman roka a birnin Donetsk na gabashin Ukraine, inda yanzu haka yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a makon jiya ke kara tangal-tangal.

Rahotanni sun ce an kai akasarin hare-haren ne a kusa da filin jiragen sama na birnin.

A kudancin kasar kuma, rundunar sojin Ukraine ta ce har yanzu 'yan tawaye na ci gaba da kai hari a kan wasu yankunan da ke hannun gwamnati a kusa da garin Mariupol da ke gabar teku.

Sai dai mataimakin babban mai sa ido na hukumar tsaro ta Turai, OSCE, Alexander Hug ya ce a daidaikun wurare ne kawai ba a aiwatar da yarjejeniyar ba.

Shugabannin kasashen Rasha da Ukraine da Faransa da Jamus sun yi Allah wadai da saba yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin Ukraine.

Bayan tattaunawar kwanaki hudu ta wayar tarho, shugabannin sun yi kira da a aiwatar da matakan da aka amince a Minsk da suka hada da na tsagaita wutar.