WHO na fadakarwa kan wasu cututtuka

Image caption WHO ta ce an yi watsi da cututtukan da ke faruwa a yankuna masu zafi

Hukumar Lafiya ta Duniya ta kaddamar da wani shiri na wayar da kan jama'a a kan cututtuka 17 da ake samu a kasashe masu zafi.

A cewar hukumar, cututtukan sun shafi kimanin mutane biliyan daya da rabi a fadin duniya.

WHO na yin kira ga gwamnatoci su mayar da hankali a kan wadannan cututtuka da suka hada da tundurmi da dindimi, wadanda ke nakasa mutane, wani lokacin ma sukan kai ga kisa a kasashe masu tasowa.

Jami'in hukumar Dr Dirk Engels ya shaida wa BBC cewa yawancin wadannan cututtuka ana iya yin rigakafin su, amma bayyanar cututtuka irinsu Ebola ya sa an yi watsi da su.

Hukumar ta ce ana samun ci gaba a yunkurin da ake yi na kawar da cututtukan da ake samu a yankuna masu zafi kamar su kurkunu, wadda a yanzu masu dauke da ita ba si wuce mutane 150 ba.