'Yan Boko Haram sun kashe mutane 21 a Borno

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Mayakan Boko Haram a jihar Gombe

Hukumomi a Nigeria sun ce mayakan Boko Haram wadanda dakarun kasar suka fatattaka sun kashe mutane 21 a kusa da garin Chibok.

Wani shugaban al'umma a yankin Chibok na jihar Borno, ya ce 'yan Boko Haram din kuma sun kona gidaje da dama a kauyen.

Kakakin rundunar sojin Nigeria, ya ce mayakan Boko Haram din sun arce ne sakamakon luguden wuta da ake musu ta sama da kuma ta kasa a dajin Sambisa.

Shugabannin tsaro daga Nigeria da kuma kasashen Chadi da Nijar da Kamaru da kuma Benin za su yi wani taro a mako mai zuwa domin tattauna yadda za su ci gaba da murkushe 'yan Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 a Nigeria.