Wayoyin salula ke sa dauke wuta a Ghana — Mahama

Mahama ya ce wayar salula ta fi mutanen kasar yawa.
Bayanan hoto,

Mahama ya ce wayar salula ta fi mutanen kasar yawa.

Shugaban kasar Ghana John Mahama ya ce kasar tana fuskantar matsalar yawan dauke wutar lantarki ne saboda yawaitar masu yin cajin waya.

A lokacin da yake yi wa 'yan Ghana mazauna kasar Gambia jawabi lokacin da ya kai ziyarar aiki, Mr Mahama ya ce adadin wayoyin da ake amfani da su kasar ya haura yawan al'umar kasar.

A cewarsa, "Ghana na da mutane miliyan 25, amma alkaluma sun nuna cewa masu wayar salular sun kai miliyan 27 , kuma kullum sai an caza wadannan wayoyi, ba dare ba rana; hakan ne ya sa ba a samun wutar lantarki".

A farkon makon nan ne dai babbar jam'iyyar kasar, NPP ta gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a kan yawan dauke wutar lantarki, tana mai cewa ya kamata shugaban kasar ya yi jawabi kan dalilin da ke sa wa ana dauke ta.