Ba ma bukatar soji a rumfunan zabe — Majalisa

Ginin majalisar dokokin Nigeria. Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption 'Yan majalisar sun ce ba sa bukatar ganin ko soja guda arunfunan zabe.

Majalisar wakillan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin kasar da kada ta tura jami'in soja ko daya zuwa rumfunan zabe a yayin manyan zabukan kasar da za a gudanar a watan gobe.

A yayin zamanta na ranar Alhamis, majalisar da gagarumin rinjaye ta ce tura sojojin zuwa rumfunan zabe ya saba wa sashe na 217 na kundin tsarin mulkin kasar kamar yadda hukuncin wata kotun tarayya da ke zama a birnin Sakkwato ya tabbatar.

'Yan majalisar sun ce ba sa bukatar soja ko guda, amma su na bukatar jami'an 'yan sanda wadanda aka amince su yi cudanya da al'uma a lokacin zabe.

Haka nan sun ce filin zabe ba filin yaki ne da sojoji za su je da bindigogi ba, abin da soja zai yi a filin zabe shi ne ya je ya kada kuri'arsa a matsayin sa na dan kasa.

Sai dai wasu 'yan majalisar na ganin cewar ko da hakan ba ya cikin kundin tsarin mulkin Nigeria, aikin tsaro ba za a bar dan sanda kadai ko soja ba, domin akwai wuraren da dole a bukaci sojoji, misali yadda a yanzu sojoji ke tsayawa a wuraren binciken ababen hawa alhali aikin 'yan sanda ne. A cewarsu kamawa ta ke har sojoji su shiga cikin ayyukan 'yan sanda.