Mutane 158 da Boko Haram ta sace sun koma gida

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumomi sun ba da shawarar kada mutanen su koma Katarko saboda dalilai na tsaro

Hukumomi a jihar Yobe a Najeiya sun ce sun hada mutane 158 wadanda Boko Haram ta sace a kauyen Katarko da iyalansu.

Mafi yawa daga cikinsu dai mata ne da kananan yara, kuma sun samu kubuta ne a watan Janairun da ya gabata.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Yobe, Alhaji Musa Dawa ya ce " Jami'an tsaro ne suka kwato su, amma lamari na jami'an tsaro ba za su iya baka bayani cikakke ba, amma muna kyautata zaton an kai farmaki ne su kuma 'yan Boko Haram suka gudu, su kuma suka kamo wadannan mutane suka taho da su."

Inda ya kara da cewa 62 daga cikin mutanen matan aure ne, yayin da 15 daga cikin 62 kuma an kashe mazajensu, sauran kuma mata ne da suke da 'ya'ya biyu zuwa hudu.

Ya zuwa yanzu babu tabbaci ko su ke nan mutanen da Boko Haram din ta sace a watan Disambar bara a kauyen ko kuma akwai wasu da suka rage.

Alhaji Musa ya kara da cewa an tabbatar da koshin lafiyarsu kafin a mika su ga 'yan uwansu a ranar Alhamis.