YouTube zai kaddamar da manhajar yara

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Manhajar zata bai wa iyaye damar tantance abubuwan da yara za su sanya a YouTube

A ranar Litinin shafin YouTube zai kaddamar da wata sabuwar manhaja ta yara domin basu damar amfani da shafin ta yadda ya dace.

Manhajar mai suna "Youtube Kids" tana da hanyoyin bai wa iyaye sararin tantance abubuwan da yara zau rika sanya wa a YouTube.

Manhajar zata rika aiki ne daban da ta YouTube, kuma a Amurka ne za a fara amfanni da ita, kafin daga baya a fara aiki da ita a Burtaniya.

Kakakin cibiyar Charity ya ce "tabbatar da yara suna yin abinda ya dace a intanet shi ne babban kalubalen kare yara a wannan zamani. Saboda haka yana da kyau shafin YouTube ya bullo da manhajar YouTube Kids".

"Ina da tabbacin cewa iyaye da yawa za su yi marhabin da wannan manhaja, musanman wadanda suke so kada 'ya'yan su su rika ganin abubuwan da basu da ce ba" Kakakin ya ce.

Manhajar zata kunshi abubuwa guda hudu: wasannin nishadi da wakoki da fannonin karatu da bincike.

Kazalika, kyauta za a rika samun manhajar, sai dai a na'urorin Android ne masu amfani da runbun Google za a rika samun ta.