Gobara ta tashi a wani dogon gini a Dubai

Hakkin mallakar hoto
Image caption An kashe wa ginin dubban miliyoyin daloli

An kwashe dubun- dubatar mutane a Dubai bayan wuta ta tashi a daya daga cikin gine- ginen gidaje mafi tsawo a duniya dake kasar.

Wani wanda ya shaida lamarin ya fadawa BBC cewa wutar wacce ta soma a kusan hawa na hamsin na dogon ginin a Dubai Marina, ta yi saurin bazuwa sama, amma hukumomin kashe gobara suka yi nasarar shawo kanta.

Babu wanda ya rasa kansa ko ya ji ciwo sakamakon tashin gobarar

Bidiyo da kuma hotunan da aka sanya a shafukan sada zumunta sun nuna wutar tana tashi a cikin ginin, da kuma zubar baraguzai a kasa.

Dogon Ginin mai hawa 75, yana da tsayin fiye da motoci 300, kuma an bude shi ne shekaru hudu da suka gabata.