Muna son komawa gida - Mutanen Gamboru

Image caption Al'ummar garin Gamboru-Ngala suna son koma wa gida

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na nuna cewa al'ummar garin Gamboru-Ngala wadanda suke gudun hijra a Fotokol da ke kasar Kamaru, sun kai wata ziyarar gani da ido zuwa garin, bisa rakiyar sojin kasar Chadi.

Bayanai kuma sun ce duk da cewa dukiyoyi sun salwanta, amma har yanzu akwai dan abin da ba a rasa ba.

A farkon watan nan ne dai sojojin kasar Chadi suka kwato garin na Gamboru-Ngala daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram, bayan dauki-ba-dadi da aka gwabza, a inda sojojin suka ce sun kashe daruruwan 'yan kungiyar.

Amma har yanzu ba a ba wa mutane damar komawa garuruwan ba, bisa dalilan hasashen cewa 'yan kungiyar ka iya dawo wa su kuma shammaci mutane.

Sai dai kuma al'ummar garin na Gamboru masu neman mafaka a Fotokol din sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ba su damar koma wa zuwa garin nasu na dindindin.