Girka:Akwai matsaloli a gaba inji Tsipras

Firaministan Girka Alexis Tsipras Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firaministan Girka Alexis Tsipras

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma a ranar Juma'a wajibi ne ya mika jadawalin garanbawul ga kasashen masu bada rance domin amincewa kafin a tsawaita wa kasar wa'adin biyan bashin da watanni hudu.

Firaministan Girka Alexis Tsipras ya fada a ranar Asabar din nan cewa yarjejeniyar da aka cimma da kasashe masu amfani da kudin euro na tsawaita wa'adin biyan bashin babbar nasara ce.

Ana yiwa yarjejeniyar kallo a matsayin tursasawa akan Firaministan wanda ya ci zabe da alkawarin sauya matakan tsuke bakin aljihu na kasafin kudin kasar.

Ya yabawa yarjejeniyar da cewa gagarumin mataki ne na kawo karshen matakan tsimi sai dai yace akwai babban kalubale a gaba.