Ebola: Za a dage dokar hana fita a Liberia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana samun gagarumar raguwar masu kamuwa da Ebola a Liberia

Gwamnatin Liberia ta ce zata dage dokar hana fita daga gidaje daga dare zuwa wayewar gari da aka sanya a fadin kasar saboda cutar Ebola.

A cikin watan Agustan bara ne gwamnatin kasar ta sanya dokar, farko daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safe, amma daga baya aka mayar da dokar ta fara aiki daga karfe 12 na dare.

Dokar daya ce daga cikin tsauraran matakan da gwamnatin Liberiya ta dauka domin dakile yaduwar cutar Ebola a kasar a bara.

Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf ta bayar da umurnin a bude manyan iyakokin kasar da suma aka rufe lokacin da cutar ke ganiyar yaduwa.

Makarantu sun fara bude wa da kadan kadan, bayan sun shafe watanni 6 suna rufe a kokarin kawar da annobar.

Fiye da mutane dubu 9 ne cutar Ebola ta kashe a yammacin Afrika.