Moscow:Gangamin juyin juya halin Ukraine

Taron gangami a Moscow Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Taron gangami a Moscow

Juyin-juya halin na Ukraine dai shi ne ya hambarar da shugaban kasar mai goyon bayan Rasha Viktor Yanukovych daga karagar mulki.

A birnin Moscow masu zanga zangar sun yi maci suna dauke da tutar kasar Rasha da hoton shugaba Vladimir Putin suna kuma rera wakoki suna cewa "ba za mu manta ba"

Gwamnatin Ukraine da shugabannin kasashen yamma da kuma kungiyar kawancen tsaro ta NATO sun ce akwai kwakkwarar hujjar cewa Rasha na 'yan tawaye a gabashin Ukraine da makamai da kuma sojoji.

Rasha dai ta musanta zargin, ta na mai cewa duk wasu 'yan Rasha da ke cikin 'yan tawayen mutane ne 'yan sa kai.