Amurka da Burtaniya sun yi wa wani kamfani kutse

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A shekarar 2010 ne kasashen biyu suka fara kutsen

Hukumomin leken asiri na kasar Amuka da Burtaniya sun yi kutse a wani babban kamfanin samar da layin wayoyin salula domin satar wasu lambobi da zasu basu damar sauraron firar da mutane suke yi ta waya.

Tsohon jami'in leken asirin Amurka, Edward Snowden ne ya tona asirin kutsen.

Kamfanin samar da layin wayoyin salula na Gemalto na kasar Jamus ya ce bai dauki zargin da wasa ba.

Bayanai sun nuna cewa a shekarar 2010 ne hukumar leken asiri ta Burtaniya, GCHQ da kuma ta Amurka, NSA suka shirya kutsen.

Har yanzu babu daya daga cikin hukumomin biyu da ya ce uffan a game da zargin.

Sai dai hukumar GCHQ ta ce tana gudanar da dukkan ayyukanta ne bisa bin doka.