Nijar ta karfafawa sojojinta gwiwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Nijar sun shiga yaki da Boko Haram

Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou ya kai wata ziyara a jahar Diffa da ke yankin gabashin kasar, ranar Asabar, domin karfafawa sojin kasar da ke yankin gwiwa, bisa kokarinsu na dakile hare- haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Shugaba Issoufou ya ce abin da ya sa ya je Diffa shi ne domin ya gaida askarawan kasar, ya kuma basu kwarin gwiwar kare kasar da al'ummominta da kuma dukiyoyinsu.

Al'ummar Diffan dai sun yaba wa Shugaban Kasar, sun kuma bayyana gamsuwarsu dangade da kokarin da yake yi wajen ganin an kawo karshen hare-haren Boko Haram, a kasar.

Shugaban ya ziyarci rundunar soji ta 52 a garin na Diffa , daga bisani kuma ya ziyarci mutanen da hare- haren Boko Haram ya shafa a babban asibitin garin.

Boko Haram ta kai hare-hare garin Diffa a kwanakin da suka gabata.