'Faransa na ba Nijer sirrin Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ministan harkokin wajen Nijer, Mohamed Bazoum, ya ce Faransa na taimakon kasarsa da bayanan sirri kan ayyukan 'yan Boko Haram.

A hirar da yayi da Sashen Hausa na BBC a ranar Lahadi, ministan ya ce Faransa na amfani da na'urorin tattara bayanai kan ayyukan kungiyar Boko Haram, kuma tana baiwa Nijer bayanan.

Ya ce bayanan suna yi ma Nijer amfani matuka a yakin da ta ke yi da ta'addanci.

Haka kuma ya ce Faransan na daga cikin kasashen da za su taimaka wajen ganin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta bada tallafi ga rundunar hadin-guiwa wadda Tarayyar Afrika ta amince a kirkiro domin yaki da Boko Haram.

Minista Bazoum ya fadi hakan ne bayan ziyarar da ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya kai a Nijer, inda ya gana da Shugaba Mahammadou Issoufou da wasu manyan jami'an gwamnatin ta Nijer, har da Mista Bazoum din.

Kafin zuwansa Nijer dai, Minista Fabius ya ziyarci Chadi da Kamaru a rangadinsa na kasashen Afrika renon Faransa masu yakar Boko Haram.

Ya ce ya gamsu da irin kokarin da kasashen ke yi, kuma ya ce Faransa za ta ci gaba da agaza masu.

Sai dai ya ce kamata yayi Najeriya ma ta maida hankali sosai wajen magance matsalar ta Boko Haram.

Karin bayani