An kai harin bom a Potiskum

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'yar kunar-bakin-wake ta kai hari a Potiskum

Rahotanni daga birnin Potiskum na jihar Yobe a arewacin Najeriya na cewa akalla mutane shida ne suka rasa ransu, sannan kimanin 20 suka jikkata sakamakon wani harin-kunar-bakin-wake da wata mace ta kai a kasuwar wayar salula, a birnin.

Wadanda suka shaida yadda al'amarin ya faru sun fada wa BBC cewa matar ta tayar da bom din ne a lokacin da take kokarin shiga kasuwar wayar da aka fi sani da kasuwar tsaye, bayan da jami'an tsaron kasuwar suka nemi su bincike ta.

Shaidun sun ce wadanda suka jikkatan suna asibiti kuma suna samun kulawa ta musamman.

Wannan dai shi ne karo na biyu da 'yan kunar bakin wake suke kai hari kasuwar a birnin.

Kawo yanzu dai ba bu wani wanda ya yi ikrarin kai wannan harin, sai dai kuma mazauna garin sun ce harin yayi kama da na 'yan kungiyar Boko Haram.