Ukraine na cika shekara guda da juyin juya hali

Hakkin mallakar hoto Getty

Ukraine na cika shekara guda tun lokacin da aka hanbarar da shugabankasar mai goyan bayan Rasha Viktor Yanukovyc a watan Fabrairu a wani juyin juya hali.

Wasu shugabanni daga kasashen Jamus da Poland da kasashen Baltic zasu hade da Magajinsa Petro Poroshenko wajen tunawa da abubuwan da suka faru a Kiev

Za a gudanar da wani jerin gwano da ake kira 'March of Dignity' a titunan kasar, inda masu zanga zanga da dama suka mutu a lokacin wani artabu da 'yan sanda, sannan kuma a kammala da addu'oi a wani dandalin dake tsakiyar birnin.

A ranar Asabar dubbban mutane sun halarci wani gangami a Moscow domin bikin tunawa da shekara guda da abinda Rasha ta kira wani juyin mulki