Ukraine: 'Yan tawaye sun yarda su janye

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawaye a Ukraine sun amince su janye makaman atilare

Wani Janar na sojin kasar Rasha ya ce mayakan 'yan tawaye sun amince su fara janye manyan makamansu daga fagen daga a gabashin Ukraine.

Janar Alexander Lentsov ya ce shugabannin 'yan tawayen masu goyon bayan Rasha sun rattaba hannu akan wani umurni na su kammala janyewa a cikin makonni biyu.

Janye makaman atilare daga fagen daga, daya ne daga cikin jigajigan abubuwan da yarjejeniyar ta Minsk da aka cimma a makon jiya ta kunsa, sai dai hakan ya gamu da tsaiko sakamakon ci gaba da gwabza fada a wasu wurare.

Tun da farko dai, bangarorin biyu sun yi musayar firsinoni da dama da ake tsare da su.

'Yan tawayen sun mika mutane 139 'yan kasar Ukraine da suke tare da su, ya yinda hukumomin Ukraine din suka mika mayakan 'yan tawayen 52.