Kamfanin Apple zai gina karin cibiyoyi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamfanin Apple ya shahara wajen kera wayoyin salula da kwamfutoci

Kamfanin wayoyi da kwamfutocin Apple zai zuba jarin Fam biliyan daya da dubu 250 wajen gina cibiyoyin tattara bayanai a jamhoriyar Ireland da Denmark.

Za a gina cibiyoyin ne a kusa da Athenry dake yankin Galway da Viborg, tsakiyar Jutland.

Cibiyoyin za su samar da guraben aikin yi 3000, sai dai akasarin guraben a fannin ginin cibiyoyin ne.

Kamfanin Apple yana son cibiyoyin su rika amfani da lantarki da za a samu daga hasken rana ko iska.

Cibiyoyin za su kunshi manya manyan na'urori da za su bukaci lantarki wadatacciya saboda a rika sanyaya su.

Kamfanin Apple zai yi amfani da cibiyoyin a matsayin wuraren gudanar da runbun wakokin sa ta intanet da kuma na manhajoji.

Firayiministan Ireland, Enda Kenny ya bayyana yunkuri a matsayin babbar harka da mutane da yawa a yankin za su amfana da ita.