'Yan Boko Haram sun zubar da makamansu'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojoji na cin nasara a kan Boko Haram a Baga

A Najeriya, hedkwatar tsaro ta kasar ta ce sojoji na ci gaba da tattara tarin makamai iri daban daban da mayakan kungiyar Boko Haram suka gudu suka bari a Baga.

Kakakin hedkwatar tsaron Manjo Janar Chris Olukolade ya ce sojoji sun gano babura da ko dai aka lalata, ko kuma mayakan kungiyar suka gudu suka bari a garin.

Janar Olukolade ya ce an yanki soja daya da wuka, sannan an harbi wani a lokacin da sojojin suke binciken gano mayakan kungiyar da suka boye.

Ya ce ana gudanar da bincike akan wasu mutane da suka ce su mazauna garin Baga ne, domin tabbatar da cewa ba aiki suke yiwa kungiyar ta Boko Haram ba.

Sai dai a wani sakon da suka wallafa a shafinsu na twitter, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun ce har yanzu su ke rike da garin na Baga.