'Yan Boko Haram na shigar mata a Baga

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Daya daga cikin wanda rundunar ta ce yayi shigar mata

Rundunar tsaron Nigeria ta yi ikirarin kama wasu 'yan Boko Haram da suka yi shigar mata a binciken da rundunar ta yi a Baga.

Kakakin rundunar Manjo Janar Chris Olukolade, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa ya ce an gano makamai da dama a wurare daban-daban na garin Baga da 'yan Boko Haram din suka boye.

A cewarsa, a yanzu haka ana ci gaba da yin tambayoyi ga 'yan Boko Haram din da aka kama a garin Bama da sojin suka ce sun kwace.

"Tun da mun kwato Baga a yanzu dakarun sun maida hankali ne wajen kwato wasu yankunan," Manjo Janar Olukolade.

Haka kuma, rundunar sojin saman Nigeria na ci gaba da luguden wuta a maboyar 'yan Boko Haram da suka hada da Gwoza da Bama da kuma dajin Sambisa.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 a Nigeria.

A yanzu dai sojojin Nigeria da Chadi da Kamaru da Benin da kuma Nijar ne ke yaki da Boko Haram.