Boko Haram: Kwararru za su gana a Cadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram na kaddamar da hare hare a kan kasashen yankin tafkin chadi

Ranar Litinin ne masana harkokin tsaro na kasashen Hukumar Raya Tafkin Cadi, LCBC, za su yi taro a N'Djamena, babban birnin kasar Cadi, don tattaunawa a kan yadda rundunar kawancen da kasashen suka kafa za ta yi aiki.

Manufar taron ita ce zakulo hanyoyin da za a aiwatar da wadansu dabaru don yakar 'yan kungiyar Boko Haram, wadanda suka zame wa kasashen Hukumar karfen kafa.

A farko wannan watan en dai kasashen na Cadi, da Kamaru, da Najeriya, da Nijar—da ma Jamhuriyar Benin, wacce ba ta cikin Hukumar—suka gana a Yaounde, babban birnin Jamhuriyar Kamaru, inda suka cimma yarjejeniya ta karshe a kan kafa rundunar ta hadin gwiwa.

Kungiyar Boko Haram na kai hare hare a kasashen Nigeria da Kamaru da Nijar da kuma Chadi