Boko Haram: Kwararru a kan tsaro za su gana a Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram na kaddamar da hare hare a kan kasashen yankin tafkin chadi

Masana a harkokin da suka danganci tsaro na kasashen Hukumar raya tafkin Chadi za su halarci wani taro a ranar Litinin wanda zai tattauna batun yadda rundunar kawance ta sojojin da aka kafa za ta yi aiki.

Wannan taron da za a bude shi a birnin N'Djamena na kasar Chadi, zai kuma nemi tsaida hanyoyin aiwatar da dabarun yaki da 'yan kungiyar Boko Haram , wadanda suka yi wa kasashen Hukumar kawanya.

Ko da yake a shekarun baya, hukumar ta fara yunkurin kafa runduna ta soji amma kuma aka samu cikas ta bangaren Kamaru wurin bada hadin kai.

Kungiyar Boko Haram na kai hare hare a kasashen Nigeria da Kamaru da Nijar da kuma Chadi