Nijar: An sake bude kasuwar Diffa

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Nijar na fuskantar hare haren 'yan Boko Haram

A Jamhuriyar Niger an bude kasuwar tattasai da ke garin Diffa bayan rufeta da aka yi na wani lokaci biyo bayan hare haren 'yan kungiyar Boko Haram

Kasuwar dai ta fuskanci hare- haren bama-bamai ne a kwanakin baya, abunda ya tada hankalin mazauna garin na Diffa.

Akalla mutum guda ne ya rasa ransa a kasuwar, sannan wasu mutane sama da ashirin suka sami raunuka bayan fashewar wani bam a cikin kasuwar.

Kasuwar dai na samun baki daga kasashen dake makwabtaka da Nijar irin su Nigeria.

Kungiyar Boko Haram na yawaita kaddamar da hare haren ta a kan kasuwanni.