An nuna mana bamu iya ba - Galadima

Hakkin mallakar hoto apc
Image caption Janar Buhari ne dan takarar jam'iyyar APC

Daya daga cikin jigogin jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria, Injiniya Buba Galadima, ya ce tun da an nuna musu cewa ba su iya ba, shi ya sa ya dan ja gefe a kamfe din da jam'iyyar APC ke yi na tallata dan takararta na shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari.

Injiniya Buba Galadima na cikin wadanda suka taka rawa wajen kafuwar jam'iyyar, kuma yana da kusanci da Janar Muhammadu Buhari a baya, sai kuma ga shi yanzu ba a jin duriyarsa a yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar.

Ya kara da cewar "Komai na da lokaci, da da mu ake yi amma mun ja gefe--wasu na ganin cewar ba mu iya ba."

"Mu muka kafa wannan jam'iyyar, kuma ko me mutum ya samu a cikinta ko kuma ya zama muna da kamasho," in ji Galadima.

Janar Buhari zai fuskanci Shugaba Jonathan na PDP a zaben da za a yi a ranar 28 ga watan Maris.