Ana taro kan shafukan zumunta a Lagos

Image caption Shafukan zumunta na tasiri a rayuwar bil-adama a wannan zamanin

An bude taro a birnin Lagos na Nigeria kan yadda ake yin amfani da hanyoyin sada zumunta da muhawara wajen bunkasa ci gaba.

Taron na wannan shekarar zai duba yadda ake yin amfani da wayoyin salula wajen kawo sauye-sauye a rayuwar dan Adam.

Mahalarta taron za su kuma duba irin rawar da hanyoyin sada zumunta da muhawara ke takawa musamman a zaben 2015.

'Duniya ta zama daya'

Mahalarta taron na duba irin tasiri wadannan hanyoyi wajen hada kan al'ummar duniya da tabbatar da mulkin demokuradiyya.

A cewarsu, ya zama wajibi a sanya idanu kan wadannan kafofi ganin irin tasirin da suke yi wajen wanzar da mulki na gari.

A kasashe da dama ana yin amfani da wadannan hanyoyi wajen tilastawa gwamnatoci yin abubuwan da jama'a ke so.

A Najeriya, an yi amfani da wadannan hanyoyi a shekarar 2011 domin yin zanga-zargar da ta tilasta wa gwamnati sauya matsayinta sakamakon Karin kudin man fetur da ta yi.