Ma'aikatan SORAZ na zaman durshen a Niger

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu yankuna na arewacin Najeriya na samun man fetur daga Nijar

A jamhuriyar Nijar ma’aikatan matatar mai na SORAZ da ke Damagaram na zaman durshen a cibiyar kamfanin.

Yajin aikin na su dai ya janyo ayyuka sun tsaya cik a matatar.

Ma’aikatan fiye da 400 na nuna rashin amincewarsu ne da matakin da shugaban matatar kuma dan kasar China ya dauka na kin amincewa da yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati.

Ma’aikatan na SORAZ dai na kuma son karin albashi tare da sama musu wata doka da za ta kayyade tsarin aiki a matatar.

Jamhuriyar Nijar ta fara hako danyen mai tare da sarrafa shi a shekarar 2011.

Kuma baya ga arzikin mai da ta gano a 'yan shekarun bayan-bayan nan, kasar na da arzikin ma'adanin uranium.