'Amfani da sirinji mara tsafta na janyo yaduwar cututtuka'

Image caption Wasu na amfani da sirinji fiye da sau daya a kan marasa lafiya

Kungiyar lafiya ta duniya WHO zata kaddamar da wani shiri a ranar Litinin domin daukar matakan rage cututukan da ake samu ta hanyar amfani da sirinji marasa tsafta.

Bincike ya gano cewa amfani da sirinjin da suka gurbata ne ke janyo laurorin HIV da kuma ciwon koda a kowacce shekara

A wani kauye guda daya a Cambodia mutane sama da 270 ne akayi imanin cewa sun kamu da cutar HIV saboda wani wanda ba ma'aikacin lafiya bane ya yi ta amfani da sirinji kwaya daya tal ba sau daya ba, ba sau biyu ba, akan marasa lafiya, hakan kuma ya janyo bazuwar cututuka.

WHO zata bukaci amfani da sirinji kwaya daya sau daya, wanda take fatan hakan zai kasance tsarin amfani da sirinji zuwa shekara 2020