Dattawan Borno na so su ziyarci wuraren da soji suka kwato

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Wasu kasashen Afrika na ci gaba da nuna goyon bayansu kan yaki da Boko Haram

Dattawan jihar Borno a Najeriya sun yi kira ga rundunar tsaron kasar ta shirya wani rangadi da zai basu damar ziyarar wuraren da suka kwato daga hannun kungiyar Boko Haram.

Haka kuma sun nemi shugabannin al'umma da kuma 'yan jarida su shiga tawagar da zata ziyarci yankunan.

Dattawan jihar ta Borno sun kuma yaba wa rundunar tsaron kasar bisa yakin da take yi da kungiyar Boko Haram.

Ko da yake sun jinjina wa dakarun Chadi da Kamaru da kuma Nijar game da namijin kokarin da suka yi na tunkarar 'yan kungiyar, suna masu cewa lallai sun nuna kauna ga Najeriya.

Cikin garuruwan da rundunar tsaron Najeriyar ta yi ikirarin karbo wa sun hada da Munguno da Marte da Baga da Dikwa, sai Malam Fatori da Gamboru wanda dakarun Chadi suka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.