Boko Haram: Sojojin Nijar biyu sun mutu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Nijar na daga cikin dakarun da ke yaki da Boko Haram

Rundunar sojan Nijar ta tabatar da mutuwar sojojinta biyu bayan da motar da suke ciki ta taka wata nakiya da suke zargin 'yan Boko Haram sun binne a garin Bosso.

Kakakin sojan na Nijar, Kanar Ledru Mustapha wanda ya tabbatar da mutuwar sojojin biyu, ya kuma ce wasu mutanen hudu sun jikkata.

A halin yanzu ya ce suna amfani da wasu na'urori domin tantance ko akwai wasu karin nakiyoyin da aka binne.

Garin Bosso da ke jihar Diffa a jamhuriyar Nijar na daga cikin wadanda ke fama da hare haren 'yan Boko Haram a baya bayan nan.