Bam ya hallaka mutane 17 a Potiskum

Hakkin mallakar hoto
Image caption Inda bam ya fashe a Gombe a watan da ya wuce

Rahotanni daga garin Potiskum na jihar Yobe a Nigeria sun ce wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a cikin wata motar haya lamarin da ya hallaka mutane 17.

Wani mutumi ya shaida wa BBC cewa ya ga gawawwaki 13 a asibitin Potiskum sannan kuma wasu 35 sun samu raunuka.

Motar hayar ta yi lodi ne a tashar Dan-Borno inda za ta dauki fasinjojin daga Potiskum zuwa Kano.

Hakan na zuwa ne bayan da a karshen mako wata 'yar karamar yarinya ta tada bam a cikin wata kasuwa a Potiskum din inda mutane da dama suka rasu.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 a Nigeria.