Shekara guda bayan kisan gillar Buni Yadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kone kusan baki daya makarantar

A ranar Laraba ne aka cika shekara guda cif da kisan gillara da kungiyar Boko Haram ta yi wa wasu dalibai maza 29 a makarantarsu da ke garin Buni-yadi a jihar Yobe a Nigeria.

Lamarin ya faru ne bayan 'yan kungiyar sun afka wa kwalejin gwamnatin tarayya cikin dare, inda suka yanka daliban da suke barci a dakunan kwanansu.

Haka kuma kun giyar ta Boko Haram ta yi awon gaba da wasu dalibai, wadanda kawo yanzu babu labarinsu.

A lokacin harin dai 'yan Boko Haram din sun tara dalibai mata, inda suka ce su tafi su je su yi aure.

An kai wannan hari ne 'yan sa'oi bayan janye jami'an tsaro da ke kusa da makarantar.

Garin na Buni-Yadi na ci gaba da kasancewa a karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram.

Kungiyar ta Boko Haram ta kai hare-hare kan makarantu da dama a arewa maso gabashin gabas, amma sace 'yan mata sama da 200 daga makarantar Chibok shi ya fi jan hankalin duniya.