Bam: Mutane 26 na ci gaba da jinya a Kano

Image caption Daya daga cikin wadanda harin bam din ya rutsa da su

Kimanin mutane 26 ne ke ci gaba da karbar magani a asibiti a birnin Kano a Nigeria sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a ranar Talata a wata tashar mota da ke birnin.

Mutanen dai sun hada maza 22 da kuma mata 4.

Lamarin ya janyo mutuwar mutane 12 a harin bom din da aka kai a tsohuwar tashar motar Kano Line, wacce aka fi sani da Karota Motorpark.

Duk a rana guda kuma, aka kai hari a wata tashar mota a Potiskum inda mutane 17 suka rasu.

A na shi bangaren shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce "reshe ya juye da mujiya" a fafatawar da ake yi da kungiyar Boko Haram kuma gwamnati za ta samu nasara.