Mutane da yawa ba su samu katin zabensu ba

Zaben Nijeriya
Image caption Zaben Nijeriya

A Nijeriya, jama'a da dama na ci gaba da korafin cewa har yanzu ba su samu katunan zabensu na din-din-din ba, yayinda ake shirin gudanar da manyan zabukan kasar a watan gobe.

A watan jiya ne dai dama aka shirya gudanar da zabukan amma aka dage saboda dalilai na tsaro, kuma sakamakon haka hukumar zabe ta kasar ta tsawaita lokacin karbar katunan zaben zuwa ranar takwas ga watan gobe.

To amma duk da haka, har yanzu akwai unguwanni ko rumfunan zabe da ko mutum guda bai samu katinsa na din-din-din ba a wasu jihohin kasar.

Al'ummar Fulani makiyaya da ke dazuzzuka a sassa dabam-dabam na kasar, su ma wani bangare ne na dimbin mutanen da ake sa ran za su kada kuri'unsu a lokacin babban zaben da ke tafe.

A hirar da wasu Fulanin dake zaune kudancin kasar suka yi da BBC sun bayyana cewar suna kokarin mallakar katunan zaben.

Karin bayani