Harin kunar-bakin-wake a tashar Biu

Daya daga cikin hare-haren da Boko Haram ta kai a wata kasuwa a Maiduguri Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A baya Boko Haram ta dauki alhakin hare-hare irin wannan da aka kai a wata kasuwa a Maiduguri

Rahotanni daga garin Biu na Jihar Borno a arewacin Nigeria sun ce wasu bamai-bamai biyu sun tashi sun kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan goma.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata tasha da ke wajen garin.

Wani wanda ya ce yana kusa da wurin lokacin da abin ya faru ya shaida wa BBC cewa 'yan kunar-bakin-wake ne mace da namiji suka tashi bama-baman.

A cewarsa, an tsayar da mutanen biyu ne a wani wuri inda aka shimfida tabarma ana binciken kayan duk wanda ya shiga garin, sai macen ta tashi bam din da ke jikinta, al'amarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama ya kuma raunata dan kunar-bakin wake na biyu.

Ihun da dan kunar-bakin-waken na biyu ya yi, yana neman taimako, inji mazaunin garin na Biu, ya sa mutane suka ruga wurinsa, amma da ya daga hannu sai aka ga bama-bamai a daure a jikinsa; hakan ya sa kowa ya ja baya.

Bayan 'yan mintuna ne sojoji suka isa wurin, suka harbi bam din sau biyu sannan ya tashi.

Wani mazaunin garin kuma, wanda ya shaida wa BBC cewa kawunsa na cikin mutanen da suka rasa rayukansu, ya ce ya ga an debi gawarwaki a motocin matasan da aka fi sani da Civilian JTF.

Har yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba game da faruwar al'amarin, kuma zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Sai dai kuma kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare irin wannan a yankin arewa maso gabashin Nigeria, da ma wadansu sassan kasar.

Ko a shekaranjiya Talata ma an kai hare-haren kunar-bakin-wake a biranen Kano da Potiskum.