Boko Haram: Jonathan ya ziyarci Mubi da Baga

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An da de ana cece-kuce kan rashin kai ziyara yankin arewa maso gabashin Nigeria da rikicin Boko Haram ya daidaita, da shugaba Jonathan ya gagara zuwa.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kai ziyara biranen Mubi da Baga a wani matakin na kara wa dakarun kasar kwarin gwiwa.

Sanarwa daga fadarsa, ta ce shugaban ya jinjinawa dakarun saboda kokari da juriya da suka nuna wajen kwato wasu garuruwa daga hannun 'yan Boko Haram.

Mr Jonathan ya ce reshe ya soma juyawa da mujiya a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

Kwamitin yakin neman zaben Shugaban Nigeria ya musanta zargin da wasu ke yi, cewa ziyarar da shugaban kasar ya kai jiya Alhamis zuwa garin Baga dake jihar Borno da kuma garin Mubi a jihar Adamawa wadanda sojojin Nigeria suka karbe daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram na da nasaba da siyasa.

Shi dai Shugaba Jonathan ya ce wannan nasara da sojojin kasar suka samu ta tabbatar da cewa gwamnatin a shirye take ta kare duk wani yanki na Nigeria.

Alhaji Isa Tafida Mafindi, shi ne mataimakin shugaban kwamitin yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar ya kuma shaidawa BBC cewa ziyarar wani mataki ne na karfafa gwiwa ga sojojin kasar ba wai don siyasa ba.

Ziyarar ta ranar Alhamis na zuwa ne bayan lokacin mai tsawo ana caccakar Mr Jonathan a kan cewar bai mai da hankali wajen ceto al'ummomin da Boko Haram ke addaba ba.

Kafin gwamnati ta mai da hankali wajen yaki da Boko Haram, kungiyar ta kwace iko da garuruwa da dama a jihohin Yobe da Borno da kuma Adamawa.