Mutane 18 ne suka mutu a harin Jos

Wasu da harin bam ya rutsa da su
Image caption Birnin Jos dai ya dade ya na fuskantar tashe-tashen hankula ma su nasaba da addini da kabilanci

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Najeriya na cewa mutane da dama da harin bama-bamai suka raunata na ci gaba da jinya a asibitoci daban-daban.

Yayin da kuma ake kokarin jana'izar wadanda suka mutu.

Bayanai dai sun nuna cewa bama-baman guda uku sun tashi a wasu tashoshin mota guda biyu da ke kusa da juna a kan hanyar Bauchi a cikin birnin na Jos.

Kuma ana jin wasu ne da ke gudu a cikin mota suka jefa bama-baman kana suka tarwatse.

Wani da ya ziyarci inda bama-baman suka tashi ya shaida wa BBC cewa a cikin wadanda suka rasa rayukansu har da dan sanda mai ba da hannu a bakin titi.

An dai tsaurara matakan tsaro sosai a ciki da wajen garin na Jos, tare da bincike, sai dai kawo yanzu ba su yi nasarar cafke ko mutum guda ba.

Hukumomin Najriya na ganin karuwar hare-haren da ake samu a arewacin kasar alamu ne da ke nuna cewa mayakan na Boko Haram na fuskantar matsin lamba daga dakarun tsaron kasar da na kasashe makwafta.