An kashe marubucin shafukan intanet a Bangladesh

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ita ma matar Mr. Roy ta samu raunuka a lokacin harin

An hallaka wani marubuci a shafukan intanet Ba Amurke dan asalin kasar Bangladesh saboda ra'ayoyinsa na rashin yarda da mahalicci.

Wadanda suka kashe Avijit Roy sun yi amfani da adda wajen sassara shi a lokacin da ya ke ziyara a Dakha, babban birnin kasar.

Mr. dai na zaune ne a Amurka, amma ya kai ziyara Bangladesh tare da matarsa domin halartar wani bajakolin litattafai a Dakhar.

Kafin kisansi ya fuskanci barazanar kisa saboda bayyana ra'ayin rashin yarda da cewa akwai Ubangiji wanda ya sabawa addinin Musulunci.

'Yan sanda sun ce suna bincike kan kisan na Mr. Roy.

Shekaru biyu ke nan da aka hallaka wani marubucin shafukan intanet, Ahmed Rajib Haider saboda sukar masu tsattsauran ra'ayi.