An amince da tsawaita dokar ta-baci a Diffa

Shugaba Muhammadou Issoufou
Image caption Gwamnatin Nijar ta lashi takobin ganin bayan mayakan Boko Haram a kasarta.

A Jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta ba gwamnati izinin tsawaita dokar ta-baci da watanni uku a jahar Diffa .

Dokar ta fara aiki ne tun daga rnar Alhamis bayan wa'adi na farko na kwanaki 15 da majalisar ta ba gwamnatin wanda ya zo karshe a cikin daren ranar Laraba da ta gabata.

A cewar hukumomi dokar ta-baci ta farko ta taimaka jami'an tsaro sun kama mutane masu dumbin yawa da ake kyautata zaton suna da alaka da kungiyar Boko Haram.

Jamhuriyar Nijar dai ta bi sahun makwabciyarta Nigeria wajen fuskantar hare-haren mayakan Boko Haram, sai dai gwamnatin kasar ta lashi takobin dakile ayyukan 'yan ta'addan a ciki da wajen kasarta.