'Gwamnati da gan-gan ta ki yaki da Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu na ganin ziyarar shugaba Jonathan da hafsan sojin kasa zai karawa sojoji kwarin gwiwa

Kungiyar dattawan arewacin Nigeria ta Northern Elders Forum, ta zargin gwamnatin kasar da cewa da ganagan ta ki daukar matakan dakile kungiyar Boko Haram da gangan.

A cewar kungiyar ganin yadda a yanzu dakarun tsaron Najeria da hukumomi suka yunkara domin yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, yasa ta ce da gangan gwamnati ta bar tarzomar ta dauki shekaru da dama ana yi.

Jagoran kungiyar dattawan, farfesa Ango Abdullahi ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, inda ya nuna shakku game da dalilan matsalar tsaro da hukumomin tsaro suka bayar, wanda ya kai ga dage babban zaben kasar.

An dai kwashe shekaru shida ana rikicin Boko Haram a kasar, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 13,000 a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International.

Kungiyar dattawan ta ce tana fatan nasarar da ake bayyanawa a baya-bayan nan zata tabbata gaskiya domin kawo karshen tarzomar baki daya.

Sai daishugaba Goodluck Jonathan ya ce yana da kwarin gwiwa cewa sojojin za su ci gaba da jajircewa a yakin da suke yi da 'yan Boko Haram.

A baya dai hukumomin Najeriyar sun bayyana rashin isassun makamai a matsayin babban abin da ke yin karan tsaye a yaki da kungiyar ta Boko Haram.

Haka kuma wasu na ganin taimakon da sojoji na makwabtan kasashe ke bayarwa na taimakawa wajen nasarorin da ake samu.

Rundunar tsaron ta Najeriyar dai tace a yanzu ta kwato garuruwan da ke hannun 'yan Boko Haram da suka hada da Baga da Marte da Munguno da Madagali.