Boko Haram: Sojojin Nigeria sun kwato Madagali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sai dai wasu 'yan kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan arewacin Najeriya

Shalkwatar tsaron Najeriyar ta ce sojojin kasar sun kwato garin Gulak na karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa da kuma garin Bara na karamar hukumar Gulani a Jihar Yobe.

Sojojin sun samu nasarar ne bayan kwashe kwanaki biyu suna gwabza kazamin fada da 'yan kungiyar ta Boko Haram,

Rundunar tsaron ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter.

Sakon ya ci gaba da cewa an kama makamai daban-daban da suka hada da harsasai da kuma motoci sannan kuma an lalata wasu.

Inda sakon ya kara da cewa a yanzu haka ana ci gaba da bincike tare da killace Gulak da garin Bara.

Hakan dai ya zo ne bayan da a cikin makon nan rundunar sojojin Najeriyar ta ce ta kame garuruwa da dama daga hannun 'yan Boko Haram da suka hada da garin Baga.

Shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kai ziyarar ba zata zuwa Baga da Mubi, inda ya gana da sojojin kasar da kuma Sarkin Mubi, a wani mataki na karfafa wa sojojin da ke filin daga gwiwa a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.