An yi gangamin adawa da Boko Haram a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Garin Amchide na daya daga cikin garuruwan da Boko Haram suka kai wa hari a Kamaru

Kungiyoyin fararen hula da kuma wasu jama’ar gari ne suka yi jerin gwano a dandalin fareti na Kamaru, domin nuna goyon bayansu ga dakarun Kasar da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Gangamin na ranar Asabar a birnin Yaounde yana kuma nuna alhini ga mutanen kasar da ke zaune a lardin arewa mai nisa wadanda rikicin Boko Haram din ya daidaita.

Masu zanga-zangar da suka kunshi daruruwan matasa dai sun yi maci ne zuwa ofishin firai Ministan kasar, Philemon Yunji Yang.

Sojojin Kamarun sun yi ikirarin kashe daruruwan 'yan Boko Haram a fafatawar da suka yi da 'yan kungiyar a lardin arewa mai nisa.

Hare-haren 'yan Boko Haram ya shafi daruruwan mazauna yankin, inda suka raba wasu da muhallansu, yayin da kuma suka kashe mutane da dama.