An harbe wani babban dan adawa na Rasha

Boris Nemtsov Dan adawar Rasha Hakkin mallakar hoto
Image caption Boris Nemtsov Dan adawar Rasha

An bindige daya daga cikin manyan 'yan adawa na Rasha Boris Nemtsov har lahira a birnin Moscow.

An harbe shi ne har sau hudu a baya daga cikin wata mota da aka gitta da ita a lokacinda yake tafiya kusa da Kremlin.

Mr Nemtsov wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin Prime Minista a karkashin Shugaba Boris Yeltsin a shekarun 1990, yana daya daga cikin masu sukar Shugaba Vladimir Putin.

Yana shirya wani taron gangami ne da za a yi ranar lahadi a Moscow don nuna rashin amincewa da abinda ya kira yakin da Rasha ke yi a Ukraine.

Karin bayani