'Yan bindiga sun kashe mutane 13 a Taraba

Image caption Mutane da dama ne suka rasa rayukansu da kuma dukiyoyi a rikice-rikicen

Rahotanni daga jihar Taraba a Najeriya na cewa an kashe akalla mutane goma sha uku, yayin da wasu kusan 20 suka jikkata, a hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai a karamar hukumar Ibi.

Wani shugaban al'umma ya shaida wa BBC cewa a ranar juma'a da yamma ne 'yan bindigar suka dirar wa kauyukan Unguwar Kwalla da Mala da kashe-kashe da kuma kone-konen gidaje.

Inda a ranar Asabar da safe lamarin ya kara ta'azzara har jama'ar kauyukan suka bazama cikin daji domin tsira.

Mazauna yankin dai na zargin 'yan kabilar Taroh ne da suka fito daga jihar Filato mai makwabtaka da Taraba da kai hare-haren, amma 'yan kabilar Taroh sun musanta zargin.

Ko da yake da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba DSP, Joseph Kwaji, ya ce yana bukatar karin lokaci domin ya tattaro bayanai, amma wasu bayanan na cewa an tura jami'an tsaro na soji da 'yan sanda, sai dai suma suna fuskantar tirjiya daga maharan masu dauke da muggan makamai.

To sai dai kuma daya daga cikin shugabannin kabilar Taroh a kudancin jihar Filato wadanda ake zargi da kai hare-haren, Mista Janle Lohbut, ya musanta hannun 'yan kabilar Taroh a tarzomar.

Jihar ta Taraba musamman yankunan kananan hukumonmin Ibi da Wukari sun sha fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da kuma addini.