An gano sautin kide-kide na da illa

Wata matashiya na jin kida. Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Rahoton ya shawarci matasa su rage jin sauti mai kara.

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce miliyoyin matasa na cikin hadarin kamuwa da cutar da za ta kai su ga kurumcewa, saboda jin kide-kide, don haka an bukace su, da su dinga jin wadannan kade-kade na kasa da sa'a guda a kowacce rana.

Binciken da hukumar lafiya ta Duniya WHO ta fitar, ya gano cewa idan mutane ba su kiyayi yawan sauraron kide-kide ta hanyar amfani da abin makalawa a kunne ko Ear p a turance to su na gab da kurmancewa.

Rahoton yace matasa biliyan daya da miliyan guda ne ke cikin hadarin samun wannan matsala, saboda jin wannan kida, haka kuma kide-kiden da ake sanyawa a Kulop-Kulop da mashaya da wuraren da ake yin kade-kade da raye na matukar barazana ga lafiyar al'uma.

Kididdigar hukumar lafiya ta nuna cewa mutane miliyan 43 da ke tsakanin shekaru 12-35 ba sa jin magana tar-tar kamar wadanda ba sa jin kida kuma matsalarsu karuwa ta ke yi.

Dr Etienne Krug darakata ne a hukumar lafiya, ya shaidawa BBC cewa hukumar na kokarin wayarwa mutane kai game da illar da ke tattare jin sautin kida mai kara.

A dan haka ya bukaci mutane su dauki matakin rage muryar radiyon su a lokacin da suke jin kide-kide, haka kuma mutanen da ke shafe sa'o'i masu yawa su na jin kide-kiden tabbas su na yiwa kansu illa ne ba tare da sun san da hakan ba.

Dr Krug ya bukaci hukumomi su dauki matakin hana direbobin manyan motoci, ko jiragen kasa da na ruwa ko na sama su daina kurewa pasinjojin da ke cikinsu karar radiyo, maimakon haka su sanya muryar kasa da kashi 60 cikin 100 na karar muryar radiyon.